A UGANDAN dubun wani likita ta cika da ya dade yana yiwa mata allurar bacci domin ya samu yayi masu fyade.
Majiya mai tushe ta shaidawa Hausa Times cewa dubun likitan mai suna, Samuel Tumukuratire dan shekara (29) ta cika ne bayan da yayiwa wata matar aure ciki.
Daily Monitor ta wallafa a shafinta cewa mutum yana aiki ne a asibitin Najeera hospital dake kudancin Kampala, duk idan mata suka je asibitin sai ya yi masu dabarar cewa zai yi masu Gwajin cutar Kanjamau daga nan sai yayi masu allurar bacci yayi masu fyade
Hausa times ta gano matar ta tsinci kanta cikin laulayi watanni Uku bayan ta je asibitin sannan tasan bata sadu da namiji ba tsawon shekara guda bugu da kari kuma dama mijinta ma'aikaci ne a kasar waje baya kasar tsawon lokacin.
Rahotanni sunce bayan yan sanda sun tuhumi likitan ne ya amsa laifinsa a inda ya bayyana yadda yake yiwa mata fyade idan sunje asibiti
To mata da magidanta da fatan za'a kiyaye a gayawa uwargida tayi hattara a yayin kebancewa waje ganin likita.
Title :
Yadda Likita ya yiwa matar aure ciki daga zuwa Gwaji
Description : A UGANDAN dubun wani likita ta cika da ya dade yana yiwa mata allurar bacci domin ya samu yayi masu fyade. Majiya mai tushe ta shaida...
Rating :
5