Wani maniyyaci daga Jihar Nassarawa, ya shaida yadda jami’an kula da Alhazan Karamar Hukumar Nassarawa, da ke jihar Nassarawa su ka yi masa yankan wuya a Makka.
Garba Bakono, ya shaida cewa, mai makon su ba shi Dalar Amurka 800, sai su ka saka masa Dala 10 kacal a cikin ambulan su ka damka masa, a matsayin kudin guzurin sa.
Bakono, ya shaida a Madina, ranar Asabar cewa, an kusa rufe shi da duka a Makka, lokacin da a cikin rashin sani ya sayi kaya cikin wani kanti, ya bayar da kudin da ba su cika ba.
“To ai a lokacin ne fa na gano ashe wani jami’i mai suna Hayatu ya yi min yankan wuya. Shi ne ya raba mana kudin guzuri bayan mun shafe kwanaki hudu a filin jirgin Abuja, kafin mu taso ranar Lahadi.”
“An sha nanata mana cewa kowa ya tabbatar ya karbi kudin guzurin sa Dala 800, amma ya tabbatar an ba shi kwayar Dala 100 guda 8. Kudi sun cika kenan. To mu saboda rashin sani, ba mu maida hankali kan wannan gargadi da aka yi mana ba.’
Wakilin mu ya gano cewa ambulan din da aka ba maniyyacin ba ta dauke da sunan sa, kamar yadda ta sauran maniyyata ke da sunayen su da kuma kudin su daidai.
Allah ya yi wa Garba gamo-da-katarin haduwa da wakilin PREMIUM TIMES tare da wani jami’an Hukumar Alhazai mai jin korafin jama’a, inda nan da nan su ka kira Babban Sakataren Hukumar Alhazai, Abubakar Nalaraba a Makkah.
Shi kuma ya ce a tuntubi babban jami’an tsaron hukumar, mai suna Aliyu Aboki, wanda aka yi sa’a ya na Madina. Aboki ya ce kowane maniyyaci an rubuta sunan sa a kan ambulan mai dauke da kid’in sa, Dala 800 da kuma fasgo din sa a cikin ambulan din.
” Idan har ba a rubuta sunan sa ba, ta yaya sunan sa ya zo daidai da sunan da ke a jikin fasfo?”
“Watakila ya na cikin masu rashin farko ko na biyu, amma mun yi mamakin yadda ya zo a jigila ta uku.” Inji jami’an tsaron.
A karshe dai Aboki ya bada umarnin a gaggauta cika masa balas din sauran kudin sa, Dala 700.
Allah ya sauwaka
Source: Premium Hausa
Title :
Yadda Jami'an Alhazan Jihar Nasarawa Suka Yanke Mawani Maniyyaci Kudinsa
Description : Wani maniyyaci daga Jihar Nassarawa, ya shaida yadda jami’an kula da Alhazan Karamar Hukumar Nassarawa, da ke jihar Nassarawa su ka yi masa ...
Rating :
5