A can kauyen Kabimbiri da ke shiyyar Mukono a kasar Uganda ne a ka samu wata mata mai shekaru 37 da ta haifi 'ya'ya 38. Wannan mata mai suna Mariam Nabatanzi Barbiye ta na da baiwar haihuwa rututu, inda ta samu tagwaye sau shida, 'yan uku sau hudu, 'yan hudu sau uku ta kuma haifi daidaiku sau biyu.
Da wannan baiwa ta wannan mata mazauna kauyen su ka yi ma ta lakabi da "uwar tagwaye mai haihuwar 'yan hudu" bayan da ta yi aure tun ba ta wuci shekaru 12 a duniya ba.
Mariam ta bayyana wa manema labarai cewa wannan baiwar haihuwar ta gaje ta ne wajen mahaifinta, inda ta ce shima 'ya'ya 45 ya haifa amma da mata daban-daban kuma mafi yawancin haihuwar 'yan hudu ne.
Rahotanni sun bayyana cewa Mariam ba ta yi sa'ar miji ba, inda ta ce mijinta ba ya wani kula da ita da kuma yaran da haifa don wasu daga cikin 'ya'yan na ta ma ba su san shi ba saboda rashin zama.
Babban dan Mariam, Charles Musisi, wanda shekarun sa 23 ya bayyana cewa da yawa daga cikin kannen sa ba su san kamannin mahaifin na su ba, saboda rashin zama don sai da daddare ya ke dawowa kuma ba ya dadewa yake kama gabansa.
Da wannan kalubale da Mariam ta ke fuskanta na rashin kula da yadda za ta yi da 'ya'yanta ne ta ke baiwa iyaye shawara a kan su daina yiwa 'ya'yansu aure wuri kuma mazaje su rike amanar matayensu.
Shi kuma wani likita bokan turai, cewa ya yi da an baiwa Mariam shawara tun tuni wajen dakatar ma ta da haihuwa ta hanyar toshe ma ta mahaifa duba da yadda take haihuwa baji ba gani.
Labarin wannan mata dai ya ba zu a kasar ta Uganda da makotan kasashe kamar su Tanzania inda jama'a su ke ta aikowa da taimakon su wanda zai tallafa ma ta wajen kula da 'ya'yan na ta.
Title :
Wata mata mai shekaru 37 ta yi haihuwar 'ya'ya har 38
Description : A can kauyen Kabimbiri da ke shiyyar Mukono a kasar Uganda ne a ka samu wata mata mai shekaru 37 da ta haifi 'ya'ya 38. Wannan mata ...
Rating :
5