Alkalin kotun kwastamare da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ya raba auren wata mata da ta auri maza biyu a lokaci guda.
Matar mai suna Modinat Mufutau, ta bayyana wa alkali ranar Talata a kotun Agodi cewa, ta yanke shawarar auren mazaje biyu ne don ta samu gamsuwa wajen biyan bukata, kuma ta rika samun kudin ciyar da ‘ya’yan ta uku.
Daga nan sai Modinat ta roki kotun ta raba auren ta da daya daga cikin mazan, wanda ta ce shekara 12 kenan sun a tare.
Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ya ruwaito matar ta ce ta hadu da Mufutau cikin 2005, daga nan ya dirka mata ciki, ba tare da an yi musu aure ba.
Ta kara da cewa daga farkon haduwar su, Mufutau ya zama kamar wani kamilin mutum cikakke, amma tun bayan da ya dirka mata ciki, daga nan sai ya fara tsangwama har da lakada mata duka a duk ranar da ta nemi kudin rainon cikin ya yi mata.
“Daga nan, bayan na haihu, sai na bar gidan sa, kuma ba a dade ba, sai na hadu da wani mutum bayan shekara biyu da haihuwar yara biyu tare da Mufutau.
“Bayan na bar Mufutau, sai na hadu da Saheed, shi ma na haihu da shi. Amma kuma sai Mufutau ya roke ni da mu koma kamar da. Daga nan sai na rike su biyu din.
“Haka na rika yin biyayya tsakanin su, yau ina tare da wannan, gobe wancan. Wata matsala ba ta taba shiga ba, har sai da wata rana su biyun suka hadu a gida na a lokaci daya.
“Amma dai ni a yau ina shaida wa kotu cewa a raba aure na da Mufutau, domin na gaji da shi. Ya daina ba ni kudin cefane da sauran kudaden tafiyar da rayuwar yau da kullum. Ga kuma ‘ya’ya a tsakanin mu. Rabon da ya ba ni wani abu, tun ranar da shi da Saheed su ka jibgi junan su a gida na.”
Mufutau, wanda ya na cikin kotun ake bayanin wannan bahallatsa, bai nuna kada a raba auren ba.
Sai dai shi ma ya ce: “Modinat munafikar mara kunya ce, ai ni ban taba sanin ta na dadiro da Saheed ba, har sai ranar da na same shi a cikin gidan da ta ke haya, gidan kuma ni ne ke biyan hayar sa.
“Ni abin da kawai na ke so, shi ne kotu ta ba ni dan mu nafarko da ke hannun ta, ya koma a wuri na. Kuma na yi alkawari zan rika ba ta kudin da za ta rika ciyar da dan mu na biyu da ke hannun ta.
Alkalin kotun, Munkaila Balogun tare da taimakon Aare Samotu da Ganiyu Alao, sun amince da raba zaman dadiron da su ke yi, sannan kuma an yarda Mufutau ya rike dan su na farko, kana kuma ya rika bai wa Modinat naira N3,500 duk wata a matsayin kudin kula da dan su na biyu da ke hannun ta.
A karshe kuma kotu ta gargade su da kada a kara jin wata fitina ta kunno kai a tsakanin su.
Allah ya kyauta
Source: premium Hausa
Title :
Wata Kotu Ta Raba Auren Wata Dake Auren Maza Biyu A lokaci Daya
Description : Alkalin kotun kwastamare da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ya raba auren wata mata da ta auri maza biyu a lokaci guda. Matar mai suna ...
Rating :
5