Na gari dai ba su karewa domin kuwa wasu maniyyatan jihar Sokoto sun yi tsintuwar makudan kudi a kasa mai tsarki kuma sun maishewa mai wannan kudade abin sa.
Wasu maniyyata biyu na jihar Sokoto sun yi tsintuwar kudi na Dalar Amurka 700, Sefa ta Nijar 15,000 da kuma riyal na Saudiya 137 a kasa mai tsarki, kuma sun mayarwa da mai shi wanda shima maniyyacin jihar ne.
Daya daga cikin maniyyatan, Dauda Ibrahim, daga karamar hukumar Gwadabawa dake jihar ta Sokoto, ya bayyana cewa, sun yi tsinyuwar wannan kudin ne a hawa na biyu na Otel din Rhoda, inda daman nan masauki da aka tanadarwa maniyyatan jihar Sokoto wanda yake unguwar Masfalah a can kasa mai tsarki.
Mallam Dauda, wanda manomin albasa ne, ya bayyanawa manema labarai na DAILY TRUST cewa, da kyar ya samu ya cika kudin kujerar sa ta tafiya aikin Hajjin bana, amma tsintuwar wannan kudi bat sanya shi ya so zuciyar sa ba
Source:Naij Hausa
Title :
Wasu Maniyata Biyu Yan Jihar Sokoto Sun Tsinci Makudan Kudi A Kasa Mai Tsarki
Description : Na gari dai ba su karewa domin kuwa wasu maniyyatan jihar Sokoto sun yi tsintuwar makudan kudi a kasa mai tsarki kuma sun maishewa mai wanna...
Rating :
5