Kotun sauraren kara dake Mapo jihar Oyo ta warware auren dake tsakanin wani magidanci mai suna Kabir Bakare da mai dokinsa Fumilola saboda zargin aikata lalata da wasu mazan a waje.
Kabir Bakare ya fada wa kotu cewa duk da kokarin da yake yi na kula da iyalensa amma Fumilola ta gwammace ta bi wasu mazan a a waje.
Ya ce makwabta da abokan arziki sun yi kokarin nuna masa halin da matarsa ke ciki sannan shi kuma ya sami tabbacin hakan da ya kamata dumu-dumu da wani daga cikin samarin ta.
Fumilola ba tace komai akan zargin da ake yi mata ba sai dai ta sanar da kotu cewa mijinta ya hanata ganin danta.
Ta kuma roki alfarmar kotun da a bata izinin kwashe sauran kayanta dake gidan Kabiru Bakare.
Alkalin kotun Ademola Odunade bayan sauraron su ya warware auren saboda rashin soyyaya dake tsakanin ma-auratan sannan ya dankawa Kabir nauyin kula da dan nasu wanda shekaransa biyu kenan a duniya.
Title :
Wani Magidanci Ya Yi Ido Hudu Da Matarsa Tare Da Wani Kato A Gidan Shakatawa
Description : Kotun sauraren kara dake Mapo jihar Oyo ta warware auren dake tsakanin wani magidanci mai suna Kabir Bakare da mai dokinsa Fumilola saboda ...
Rating :
5