Wata budurwa mai shekaru 19 ta haifi jariri wanda yazo da wani abin mamaki da ba’a saba ganinsa ba, shi dai wannan jariri haihuwarsa aka yi da juna biyu, inji rahoton Daily Trust.
Likitoci sun tabbatar da cewa wannan jariri da aka haifa a kasar Indiya, yazo tare da dan uwansa yan biyu, amma yan biyu yana zaune ne a cikin cikin wannan jariri.
A farkon watan Yulin bana ne aka fara lura da wasu kasusuwan halitta a cikin cikin wannan jariri, kamar yadda likitocin suka ce:
“A hoton bayan haihuwa da muka yi ma jaririn ne muka tsinkayi wata halitta ta rabin mutum hade da kwakwalwa, kafafu, da hannuwa cikin wata karamar mahaifa a cikin sa.
“Ba shakka yan biyu matar nan ta haifa, amma dayan jaririn na cikin jaririn da aka haifa, inda shi daya jaririn sati 13 kawai yayi yana girma, daga nan sai ya daina girma.” Inji likitan mai suna Thorat.
Bayan haihuwar wannan jariri ne a ranar 20 ga watan Yuli a asibiti dake kusa da Mumbai sai aka gudanar da aikin tiyata akan sa, inda aka cire masa wannan yan biyu nasa, kamar yadda aka ruwaito.
Wata likitan mata a asibitin, Neena Nichlani tace sau 100 kacal aka taba samun irin wannan haihuwa a duniya gaba daya, inda ake samun irinsa gida daya a duk cikin haihuwa 500,000.
Title :
Wani jariri da aka haifa ɗauke da juna biyu ya baiwa likitocin duniya mamaki
Description : Wata budurwa mai shekaru 19 ta haifi jariri wanda yazo da wani abin mamaki da ba’a saba ganinsa ba, shi dai wannan jariri haihuwarsa aka yi ...
Rating :
5