Gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade ya cika alkawarin sa da yayi wa Malaman Addinin Musulunci a Jihar inda ya ba su kudi Naira Miliyan 10 a dalilin addu'o'in da aka rika yi masa lokacin yana yakin neman zabe da kuma neman nasara a Kotu bara.
Shugaban Malaman Jihar Kabir Saad Ibrahim ya bayyanawa Jaridar Daily Trust wannan yace Gwannan bai yi kasa a gwuiwa ba kuma za su cigaba da yi wa Gwamna Ben Ayade da Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'a tare da kokarin hada kan Jama'a.
Kwanaki Gwamnan Jihar Kuros Riba Ben Ayade yace shi da mutanen Jihar sa sun dage ba dare ba rana wajen yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a ya samu lafiya.
Title :
Wani Gwamnan Kudu ya biya Limaman Musulunci makudan kudi
Description : Gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade ya cika alkawarin sa da yayi wa Malaman Addinin Musulunci a Jihar inda ya ba su kudi Naira Miliyan 10 a dalili...
Rating :
5