A wani al'amari mai nuna irin yadda wasu 'yan Boko Haram ke waswasin dorewar kungiyar da kuma halaccinta, wani dogarin tsaron wani na hannun daman Abubakar Shekau ya yi watsi da kungiyar tare kuma da yin wasu bayanai.
A cigaba da gane gaskiya da wasu ‘yan Boko Haram ke yi har su ke tuba, wani daga cikinsu da ya tuba kamar sauran, ya mika kai kuma a hirar da su ka yi da Haruna Dauda ya shaida masa cewa:
“Suna na Bara Umara shekaru na 27 kuma na fito ne daga cikin dajin Sambisa; ni dan Banki ne na shiga cikin wannan kungiyar ta Bako Haram ne lokacin da kungiyar ta shiga cikin garin Banki. A lokacin akwai wani aboki na mai suna Abu Mujahid; shi ne ya yaudare ni ya shigar da ni cikin wannan kungiya ta Boko Haram; ya ce mani ‘yan Najeriya arna ne kuma sojojinta ma arna ne; saboda haka in zo mu je bangaren Shekau saboda shi ne Musulmin gaskiya, mu je mu yi yaki mu kashe mutanen (marasa Imani).
“Da na ji tsoro zan gudu sai ya ce idan z aka gudu kashe ka za mu yi saboda ka riga ka ga asirinmu. Don haka sai ya shigar da ni. Sunan da na ke amfani da shi a dajin Sambisa shi ne Abu Mustapha; ni dogarin tsaron Gaidam ne, wanda ke kusa da Shekau; amma na yi ta zuwa yake-yake har sau shida a gaba da Bama da a Wulari da Bita da gefen Tafkin Chadi; haka kuma idan sojoji su ka shiga dajin Sambisa mu kan kai masu hari.”
Source: VOA Hausa
Title :
Wani Dan Boko Haram Yayi Nadama
Description : A wani al'amari mai nuna irin yadda wasu 'yan Boko Haram ke waswasin dorewar kungiyar da kuma halaccinta, wani dogarin tsaron wani n...
Rating :
5