Gwamnatin Venezuela ta ce dakarunta dubu 200 da kuma fararen hula dubu 700 sun bi sahun atisayen soji na ranar farko da aka yi.
An shirya atisayin ne bayan Amurka ta sanar da sanya takunkumin tattalin arziki a kan gwamnatin shugaba Maduro.
Amurka dai na zargin Mr Maduro da yin mulkin kama karya.
Shugaba Maduro ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, al'ummar Venezuela da ma dakarun kasar, za su rinka kare iyakokinmu da ma martabar kasarmu.
Tun a farkon watan da muke ciki ne, shugaba Trump ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar tura sojoji zuwa Venezuela bisa la'akari da wutar rikicin siyasar da ke ruruwa a kasar dama matsalar da tattalin arzikinta ke fuskanta.
Source: BBC Hausa
Title :
Venezuela Ta Daura Damarar Kare Iyakokinta
Description : Gwamnatin Venezuela ta ce dakarunta dubu 200 da kuma fararen hula dubu 700 sun bi sahun atisayen soji na ranar farko da aka yi. An shirya a...
Rating :
5