Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta wgama shiri domin kai ziyara jihar Imo a yau Laraba, 2 ga watan Agusta domin halartar taron watan Agusta da matan jihar ke yi a duk shekara.
Mai ba da shawara na musamman ga gwamnan jihar, Rochas Okorocha akan harkokin mata, Dr Nnenna Ezebuiro ce ta sanar da haka a taron manema labarai a Owerri babban birnin jihar.
A cewarta bayan uwargidan shugaban kasar, matan gwamnonin jihohi 35 dake fadin kasar zasu hallara a wajen taron.
Taron zai mayar da hankali ne akan hadin kan kasar, maimakon samar da abubuwan more rayuwa, saboda a cewar Ezebuiro, abunda kasar ke bukata kenan a yanzu haka.
Title :
Uwar Gidan Shugaban Kasa Zata kai Ziyara Jihar Imo
Description : Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta wgama shiri domin kai ziyara jihar Imo a yau Laraba, 2 ga watan Agusta domi...
Rating :
5