Tare Da Dubban Magoya Bayansa Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar 'Green Party'
Tsohon gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda tare da dubban magoya bayansa sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ta 'Green Party Of Nigeria' (GPN).
Darakta yada labaran tsohon gwamnan na Bauchi, wato Bashir Umar, ya bayyanawa RARIYA cewa sama da shekara guda kenan Malam Yuguda ya bar jam'iyyar PDP amma sai a ranar Asabar din da ta gabata ne ya sanarwa da duniya sabuwar jam'iyyar da ya koma.
Idan masu karatu za su tuna, kusan tun lokacin da wa'adin tsohon gwamnan na Bauchi ya kare a shekarar 2015, ba a cika ganin sa a al'amuran da suka jibanci tsohuwar jam'iyyar ta sa ta PDP ba.
Title :
Tsohon Gwamnan Bauchi, Malam Isa Yuguda Ya Sauya Sheka Zuwa Green Party
Description : Tare Da Dubban Magoya Bayansa Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar 'Green Party' Tsohon gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda tare d...
Rating :
5