Bisa ga dukkan alamu, sakonnin Twitter da shugaban Amurka Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence suka rubuta kan tafiyar Bannon, sun nuna cewa za su yi kewar Bannon a Fadar White House, kamar yadda masu lura da al'amura ke cewa.
“Ina so na mika godiya ta ga Steve Bannon saboda irin rawar da ya taka, ya shiga gangamin yakin neman zabe na, a lokacin ina tunkarar Hillary Clinton mara gaskiya, abin alfahari ne, na gode.” Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Shi ma mataimakin shugaban kasar, Mike Pence, ya yabi Bannon a shafinsa na Twitter a jiya Asabar, inda ya ce yana mika godiyarsa bisa abinda ya kwatanta a matsayin “yadda ya shi Bannon ya yi aiki tsakani da Allah.”
Source: VOA Hausa
Title :
Trump Da Mataimakinsa Sun Fara Kewar Banon
Description : Bisa ga dukkan alamu, sakonnin Twitter da shugaban Amurka Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence suka rubuta kan tafiyar Bannon, sun nuna c...
Rating :
5