Wata mata ta shiga hannun hukuma sanadiyar laifin karbar kudin mazajen da su ka yi amfani da 'yar ta mai shekaru 12 kacal a duniya
Jami'an 'yan sanda na jihar Kuros-Riba sun cafke wata uwar 'ya'ya niyar, Udoaka Sunday da wasu mutum uku bisa laifin aikata alfasha da 'yar ta mai shekaru 12.
Wani makocin wannan mata da ya tabbatar da laifin Udoaka ya bayyanawa manema labarai na VANGUARD cewa, Udoaka dai ta kasance ta na karbar kudin duk wani namiji da ya yi amfani da 'yar ta wanda cikinsu har da wani tsohon soja, Effiom Okon mai shekaru 78, da kuma wasu mutanen guda hudu.
Allah ya kyauta
Source: Naij.com