Shugaban Darikar Katolika na Kaduna, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta biya diyyar coci-cocin da Boko Haram su ka lalata wa kiristoci.
Mathew Ndagoso, wanda shi ne kakakin su, shi ne ya bayyana hakan a wani taron kwana biyu da su ka shirya a Minna, babban birnin jihar Neja.
”A cikin shekaru shida Boko Haram su sha kai hari a coci-cocin mu da garuruwan kiristoci a Arewacin kasar nan, amma har yau gwamnatin tarayya ba ta biya diyyar wadanda abin ya shafa ba.”
“Don haka mu na son mu shaida cewa Mabiya Darikar Katolika ba su karbi diyya ko ta kwandala gwamnatin tarayya da sunan tallafi ba ga cocin mu.”
“Nan a jihar Neja, wurin da aka fara kai wa hari tashin farko, shi ne Cocin St. Theresa da ke Madalla, a ranar 25 Ga Disamba, 2011.
”A shekarar da ta gabata kuma maharan nan sun sake kai wani harin a Cocin Katolika da ke Suleja, suka lalata dukiya mai tarinnyawa. Har yau ko jaje ba a yi mana ba.
Daga nan sai Bishop din ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta rika tausaya wa wadanda irin wannan bala’in Boko Haram ya ritsa da su.
“Lokacin da na ke Maiduguri, an lalata min gida na aka kone shi kurmus a lokacin ba na nan. Ba abin da aka tsira da shi daga gidan. Haka ma cocin mu, shi ma aka kone shi. Kuma ba wanda ya biya ni diyya ko wani tallafi daga gwamnatin tarayya ba.”
Source: premium Hausa
Title :
Shuwagabanin Katolika Sun Nemi Gwamnatin Tarayya Da Ta Biya Diyya Akan Coci Cocinsu Da Boko Haram Suka Ruguza
Description : Shugaban Darikar Katolika na Kaduna, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta biya diyyar coci-cocin da Boko Haram su ka lalata wa kiristoci. Mat...
Rating :
5