Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke taron ministoci na wannan mako, wanda shi ne na farko da aka yi tsammanin zai halarta bayan dawowarsa daga jinyar da ya shafe fiye da wata uku yana yi a Birtaniya.
Mai ba shi shawara ba musamman kan harkar yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba da safe gabannin lokacin da aka saba fara taron.
Ba a dai bayyana dalilin daukar wanan mataki ba, amma dama shugaban yana aiki ne daga gida tun bayan dawowarsa daga jinya a ranar Asabar.
Mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ne ya ce Shugaba Buharin zai dinga aiki daga gida ne saboda ana gyaran ofishinsa wanda beraye da kwari suka lalata a lokacin da ba ya nan.
Sai dai a sanarwar, Mr Adesina ya ce, Shugaba Buharin zai karbi rahoto ne daga kwamitin da aka dorawa alhakin binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa wasu jami'an gwamnati biyu, Shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasa, Chief Ayo Oke, da Sakataren gwamnati Babachir Lawal, wadanda tuni aka dakatar da su.
Source: BBC Hausa
Title :
Shugaba Buhari Ya Soke Taron Ministoci Na Wannan Satin
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke taron ministoci na wannan mako, wanda shi ne na farko da aka yi tsammanin zai halarta bayan dawow...
Rating :
5