Wasu masana tattalin arziki a Nijeriya, sun fara kalubalantar shugaban kasar Muhammadu Buhari game da farin cikin da ya nuna kan bayanin farfadowar tattalin arzikin da ministocinsa suka ce ya yi.
Dr. Nazifi Darma ya ce kamata ya yi shugaban ya tambayi ministocinsa ko mutum nawa aka samarwa ayyukan yi sakamakon ci gaban da suke ikirarin (tattalin arzikin) kasar ta samu. "Ayyuka miliyan nawa aka samar?"
"Kuma game masana'antun da suka durkushe, guda nawa ne suka bude suka ci gaba (da aiki). Kuma me suka sarrafa?", ya tambaya.
An sha jayayya don nuna cewa alkaluman bunkasar tattalin arziki da hukumomin Nijeriya kan fitar ba sa zuwa daidai da yadda ainihin rayuwar talaka take a zahiri.
Shugaba Buhari ya bayyana farin cikin ne bayan ganawar da ya yi da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da takwaranta na Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele.
Sai dai, masanin ya ce akwai bambanci tsakanin alkaluma na ci gaban tattalin arziki da kuma ainihin yadda rayuwar mutane ta kasance a wannan kasar wanda zai yi daidai da wadannan alkaluma.
Dr. Darma ya kara da tambayar wacce irin raguwa aka samu game da hauhawar farashin kayayyaki idan an kwatanta kan yadda (abin) yake kafin (yanzu)?
"Ta yadda mutane za su samu dama, su iya sayen kayayyaki da sauki, da kuma masu yawa a kan yadda suke saya da kafin shiga matsin tattalin arziki."
Kimanin shekara biyu kenan da Nijeriya ta shiga wani mummunan matsin tattalin arziki, wanda ya janyo gagarumar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Shin Buhari Ya Tambaya Aiki Nawa Aka Samawa Samari?
Description : Wasu masana tattalin arziki a Nijeriya, sun fara kalubalantar shugaban kasar Muhammadu Buhari game da farin cikin da ya nuna kan bayanin far...
Rating :
5