Rundunar Yansandan Ago-Okota ta tabbatar da kisan wata budurwa da saurayinta yayi saboda tana baiwa tsohon saurayinta lokaci shima yana zuwa zance, inji rahoton Daily Post.
DPO na yansandan yankin Yusuf Abdul ne ya tabbatar da wannan rahoto, inda yace saurayin, mai suna Victor ya hallaka budurwarsa mai suna Happinness ne saboda kishin dake damunsa yayin wani biki daya shirya mata.
An ruwaito Victor ya shirya bikin ne domn murnan zagayowar ranar haihuwarta a otel din Ago, inda ya hange ta tana tattaunawa tare da tsohon saurayinta a yayin bikin.
Title :
Saurayi ya hallaka budurwarsa kan tana zance da tsohon saurayinta
Description : Rundunar Yansandan Ago-Okota ta tabbatar da kisan wata budurwa da saurayinta yayi saboda tana baiwa tsohon saurayinta lokaci ...
Rating :
5