Mai Alfarma Sarkin Musulmi shi da Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci, sun bayyana cewa ranar 1 Ga Satumba, 2017 ce za a gudanar da Babbar Sallah a kasar nan.
Dama dai tun da farko Gwamnatin Saudi Arabiya ta bayyana wannan rana a matsayin ranar 10 Ga Zul Hajji, ranar da za a yin layya a dukkan fadin duniya.
Wannan bayani ya fito daga kamfanin yada labarai na NAN, a Sokoto, a ranar Laraba. Inda rahoton ke nuni da cewa hakan ya biyo bayan ganin sabon watan da aka yi a ranar Talata da ta gabata, watau ranar 22 Ga Agusta, 2017.
Daga nan sai Sarkin Musulmi ya yi kira ga dukkan musulmi su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a kasar nan, domin a samu kwanciyar hankali da ci gaban kasa. Ya kuma yi wa daukacin musulmi fatan alheri.
Source: premium Hausa
Title :
Ranar Daya Ga Watan Satumba Zaayi sallah Inji Sarkin Musulmi
Description : Mai Alfarma Sarkin Musulmi shi da Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci, sun bayyana cewa ranar 1 Ga Satumba, 2017 ce za a gudanar da Babbar ...
Rating :
5