A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar ministoci na farko cikin bayan tafiyarsa jinya Birtaniya, wata uku da suka gabata.
Mai magana da yawun shugaba Buhari kan yada labarai Femi Adesina ne ya wallafa shigar shugaban taron a shafinsa na Twitter.
A zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban ya karbi bakuncin kungiyar kwallon kwando ta mata ta kasar, D'Tigress.
Shugaban ya koma Najeriyar ne daga Birtaniya a ranar 19 ga watan Agusta, inda ya shafe kwana 104 yana jinya.
A lokacin da baya nan Mataimakin Shugaban Farfesa Yemi Osinbajo ne ya dinga tafiyar da al'amuran gwamnati, yake kuma jagorantar taron majalisar ministocin.
A wancan makon ne Shugaba Buharin ya soke taron, wanda aka sa ran shi ne na farko da zai jagoranta bayan dawowarsa daga jinyar.
Sai dai a ranar ce shugaban ya karbi rahoton binciken da ake yi wa sakataren gwamnatin kasar da aka dakatar kan zargin cin hanci Babachir Lawal, da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar Ayo Oke.
Ana sa ran taron na ranar Laraba zai tattauna kan batun yajin aikin da Malaman Jami'a ke yi.
Title :
Rabon Buhari Da Taron Ministoci
Description : A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar ministoci na farko cikin bayan tafiyarsa jinya Birtaniya, wata uku d...
Rating :
5