Hukumar Kwastam ta shaida wa manema labari a Lagos cewa ta kama tabar wiwi mai dumbin yawa a cikin motar jam'iar Abeokuta da ke kudancin kasar.
A ranar Talata ne wani babban jami'in hukumar na shiyyar kudu maso yammacin Najeriyar, ya ce sun kama motar ne dauke da tabar wiwi a kan iyakar kasar da Jamhuriyyar Benin.
Wani babban jami'in hukumar ya ce dole sai Jami'ar Aikin Gona ta Tarayya ta yi bayani kan yadda aka yi motarta ta dauko tabar wiwi, wacce aka haramta tu'ammali da ita a kasar.
Title :
Photos:Ankama Tabar Wiwi A Motar Wata Jamia
Description : Hukumar Kwastam ta shaida wa manema labari a Lagos cewa ta kama tabar wiwi mai dumbin yawa a cikin motar jam'iar Abeokuta da ke kudancin...
Rating :
5