Wani mutum mai suna Abraham Moses mazaunin garin Cross River wanda ake zarginsa da zama dillalin siyar da mutane ya sayar da dan mai shekara biyu Elisha Abraham ga wata mata dake zama a Uyo babban birnin Akwa Ibom akan naira N150,000 kacal.
Kwamishinan yan sandan jihar Cross River Hafiz Inuwa yace sunbi diddigin alamarin, sun nakalto daga wanda ake tuhuma ya bayyana cewa tsananin talauci da halin rayuwa ne ya sanya shi aikata wannan mummunan aika aikan.Kwamishinan yan sandan yace, a ranan 24 ga watan yuli 2017 ne matan wanda ake tuhuma ta kawo karan mijinta akan ya dauke mata yaro ba tare da sanin ta ba.
Bayan tsatssauran bincike daya gudana, an gano cewan, Abraham Moses Udoh ya siyarda dan sa Elisha ga wata matan da ba’a santa ba mazaunin garin Uyo akan naira N150,000. Amma an samu karbo naira N130,000 daga hannun shi.
Kwamishinan yankin ya kara dacewa, bincike na cigaba da gudana domin ceto rayuwar yaron daga wanda aka siyar ma. Bayan amsa laifin sa za’a bugashi kotu idan an gama bincike.
Har wayau, Udo yace yayi nadaman laifin da ya aikata amma abun takaici a gareshi shine bai san ainihin inda matar da ya sayar wa dansa take ba amma mazauniyan Iko
Source: Naij Hausa
Title :
Photos: Ya Sayar Da Dansa Akan Dubu Dari
Description : Wani mutum mai suna Abraham Moses mazaunin garin Cross River wanda ake zarginsa da zama dillalin siyar da mutane ya sayar da dan mai shekara...
Rating :
5