Hukumar kulla da gandun dajin jihar Bauchi ta sama nasarar cafke wasu gawurtatun masu haramtaciyar farauta guda 2 masu suna Amos Bitrus da kuma Danjuma Sale.
An kama mafarautan ne a yankin Tungan-Baki da ke jihar Bauchi a ranar 30 ga watan Yulin wannan shekaran, an same su ga gwagwon biri guda 1, wasu birai guda 3, bauna guda daya, Aladun daji guda 2 da kuma zabuwa guda 1.
Mafarautan kuma suna tafe da karnukan farauta guda 7, kuma sunyi yunkurin fada ma jami'an gandun dajin da fada amma basu yi nasara ba.
Rahotanni sunce Alkali ya yanke ma Danjuma hukunci shekara biyu a gidan kaso, tunda a shekaran baya an taba samun sa da laifin farauta a gadun dajin Yankari. Shi ko Amos kotu ta yanke masa hukunci zama na wata 6 a gidan kaso tunda wannan ne laifin sa na farko.
Title :
Photos :Hukuma ta cafke mutane 2 masu haramtaciyar farauta a garin Bauchi
Description : Hukumar kulla da gandun dajin jihar Bauchi ta sama nasarar cafke wasu gawurtatun masu haramtaciyar farauta guda 2 masu suna Amos Bitrus da k...
Rating :
5