Jam'iyyar PDP da ke hamayya a Najeriya ta soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kan kin kama sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal.
PDP, bangaren Sanata Ahmed Makarfi, ta ce ba dakatar da Babachir Lawal da kuma Babban Daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Ayodele Oke a yi ba, tana mai cewa kamata ya yi a kama su kamar yadda ake yi wa 'ya'yanta da ake zargi.
A wata sanarwa da kakakin bangaren na Makarfi Prince Dayo Adeyeye ya fitar, jam'iyyar ta ce ta rasa dalilin da zai sa shugaban kasar ya kafa kwamiti karkashin manyan jami'an bangaren zartarwa su binciki dan uwansu babban jami'in zartarwar.
A cewar PDP ba ta da kwarin gwiwa cewar kwamitin binciken da mataimakin shugaban kasar ke shugabanta zai yi adalci.
Ta kara da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ba ta raga wa 'yan PDP da ake zargi da hannu a aikata laifuka, don haka idan da gaske take a yakin da take yi da ci hanci da rashawa bai kamata ta tsaya gudanar da bincike ba, sai kawai ta kama Lawal da Adeyeye kamar yadda take yi wa 'yan PDP.
Jam'iyyar dai ta bukaci a kafa hukumar bincike mai zaman kanta wadda ta kunshi fitattun 'yan kasar da aka shaida da zama masu gaskiya, 'yan ba-ruwanmu kuma kwararru domin sun bincike wannan lamarin.
Source: BBC Hausa
Title :
PDP Ta Soki Buhari Kan Babachir
Description : Jam'iyyar PDP da ke hamayya a Najeriya ta soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kan kin kama sakataren gwamnatin tarayya Babachir Da...
Rating :
5