PDP Na Shirin Kunno Wutar Rikici
Tsakanin Atiku Da Sule Lamido
Jaridar Sahara Reporters ta
ruwaito cewa, kusoshin jam'iyyar
PDP na kulla makarkashiyar
kaddamar da tsohon mataimakin
shugaban kasa Atiku Abubakar a
matsayin dan takarar shugaban
kasa a karkashin Jam'iyyar PDP
kana kuma Gwamnan jihar Ekiti
Ayo Fayose a matsayin
mataimaki. Kujerar da tsohon
gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule
Lamido ya ke nema ba dare ba
rana.
Source from rariya