Kungiyoyin da dukkaninsu ke buga wasan Ligue 1 na kasar Faransa, sun cimma matsayar ce a jiya Lahadi.
Cinikin dai yasa Mbappe zai zama dan wasa na biyu mafi tsada bayan Neymar, wanda shima kungiyar ta PSG ta saye daga Barcelona a kan fam miliyan 222, a farkon watan da muke ciki.
Kafafen yada labaran wasannin Faransa sun rawaito cewa yarjejeniyar farko da Mbappen zai sanya hannu ta koma kungiyar PSG ce a matsayin aro, amma daga baya kungiyar zata maida komen nasa na din-din-din.
Source: RFI Hausa
Title :
Paris Saint-Germain ta amince ta biya kungiyar Monaco fam miliyan 180 domin sayan dan wasanta Mbappe.
Description : Kungiyoyin da dukkaninsu ke buga wasan Ligue 1 na kasar Faransa, sun cimma matsayar ce a jiya Lahadi. Cinikin dai yasa Mbappe zai zama dan ...
Rating :
5