Neymar ya caccaki daraktocin Barcelona kungiyar da ya bari ya koma Paris St Germain a matsayin wanda aka saya mafi tsada a bana.
Dan wasan na tawagar kwallon kafa ta Brazil ya yi wannan jawabin ne, bayan kammala wasan da PSG ta doke Toulouse 6-2 a gasar Faransa a ranar Lahadi, kuma ya ci kwallo biyu.
Neymar mai shekara 25 ya ce ''Na yi shekara hudu a Barcelona cikin farin ciki mun rabu cikin murna, amma ban yi shiri da daraktocinta ba''.
''A waje na bai kamata suna aiki da Barcelona ba, kuma kungiyar ta cancanci ci gaban da ya wuce wanda take da shi a yanzu''.
Neymar ya ci kwallo uku a wasa biyu da ya buga wa PSG tamaula, sai dai tun barinsa Spaniy, Barcelona ta yi rashin nasara da ci 5-1 gida da waje a hannun Real Madrid a Spanish Super Cup.
Source: BBC Hausa
Title :
Neymar ya Caccaki Darektocin Barcelona
Description : Neymar ya caccaki daraktocin Barcelona kungiyar da ya bari ya koma Paris St Germain a matsayin wanda aka saya mafi tsada a bana. Dan wasan ...
Rating :
5