Mutane sama da miliyan biyu ne suke zaune a sansanoni daban- daban dake jihar Barno dalilin rasa matsuguninsu da suka yi a sanadiyyar hare haren Boko Haram.
Mai makon samun tsaro da natsuwa ga mazaunan sansanonin sun zama wajen tashin hankali ga musamman mata saboda tsananin aikata fyade a keyi duk dare.
Wani mazaunin sansanin Dalori mai suna Baba Kura dan shekaru 67 ya ce da ya ga abin yaki ci ya ki cinyewa ya kwashe iyalansa kaf daga sansanin saboda Matsanancin aikata lalata da akeyi da mata da karfin tsiya.
‘‘Ina da‘ya’ya mata shida;uku daga cikinsu zaurawa ne sauran ‘yan mata. Kusan kowani dare za kaji ihun mata ana musu fyade a sansanin Dalori wanda hakan ya sa nake gadin ‘ya’yana kowani dare.”
Baba kura ya ce dole ya ta shi daga sansanin.
Wata mazauniyar sansanin ta ce Allah ya kubuta da ita daga harin da aka kai don yi mata fyade lokacin da wasu matasa suka kawo mata dauki bayan an bita da gudun tsiya za a danne.
Ta ce garin wannan gudu ne ta fadi har ta Karya kafadarta.
Bayan haka shugaban hukumar bada agaji na yankin arewa maso gabas Muhammed Kanar ya ce za su hada hannu da ma’aikatar al’amuran mata da kungiyar ‘Federation of Women Lawyers, (FIDA) don magance wannan mummunar anoban.
‘‘Babu wanda ya kawo karan fyaden da ake yi wa mata a sansanonin amma duk da haka za mu yi bincike.”
Ya ce hukumar NEMA ta samar da ma’aikatan kiwon lafiya da kuma jami’an tsaro domin kare mazaunan sansanonin jihar sannan ya yi kira ga mazaunan da su kai karan duk wanda ya ci mutuncin su a ofishinsu.
Source: Premium Hausa
Title :
Nakwashe Duk Iyalai Na A Sansanin Yan Gudun Hijra Saboda Fyade
Description : Mutane sama da miliyan biyu ne suke zaune a sansanoni daban- daban dake jihar Barno dalilin rasa matsuguninsu da suka yi a sanadiyyar hare h...
Rating :
5