Masu iya magana sukance 'babu nakasashe sai wanda zuciyar sa ta mutu' wani matashi mai suna Gaddafi, dan asalin jihar Zamfara wanda ya rasa kafarsa a dalilin kamuwa da cutar shan-inna wato 'Polio' a turance, amma bai bari rashin kafar nasa ya kashe nasa zuciya ba.
A yayin da wasu guragun su ka maida bara ta zama sana'arsu, Gaddafi ya dage ne wajen aikin noma domin biyan bukatun sa har ma da taimaka ma wasu. Mallam Gaddafi dai kamar yadda zaku gani a hoton da yake rike da fatanyar sa ya dage ne wajen noman shinkafa.
Shi dai saurayi Gaddafi ya rasa kafar sa tun yana karamin yaro bayan kamuwa da cutar na shan-inna, amma abin sha'awa shine halin da ya tsinci kansa bai sa ya fara bara ba kamar yadda sauran guragu keyi.
A halin yanzu bashi da aure amma yace yana sa ran yin auren nan da wani lokaci mai zuwa.
Title :
Nakasashen matashi a Zamfara ya rungumi aikin Noma
Description : Masu iya magana sukance 'babu nakasashe sai wanda zuciyar sa ta mutu' wani matashi mai suna Gaddafi, dan asalin jihar Zamfara wanda ...
Rating :
5