Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi arin ciki da farfadowar tattalin arzikin Najeriya.
Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.
Shugaban ya gana da su ne har tsawon kimanin sa'o'i biyu ranar Litinin, kamar yadda Mataimakinsa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana.
Adesina ya ce sun tattauna batutuwan manofofin kudin kasar da tattalin arziki da dai sauransu.
Shugaban ya kara jadaddawa ministocin da gwamnan CBN da cewa gyara tattalin arziki shi ne babban alkawarin da jam'iyyarsa ta yi wa 'yan kasar, kamar yadda ya ce.
Adesina ya ce shugaban ya nuna "farin cikinsa da yadda al'amura suke tafiya bayan shekara biyu da tabarbarewarsu."
Shugaban ya bukaci ministocin da su ci gaba da ba da himma don babban aikin gwamnati shi ne samarwa 'yan Najeriya saukin rayuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Naji Dadin Farfadowar Tattalin Arzikin Nigeria-Buhari
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi arin ciki da farfadowar tattalin arzikin Najeriya. Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Minis...
Rating :
5