Labarun da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni da cewa da alamu takun sakar da ke a tsakanin manyan jarumai mata a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi na shirin daukar sabon salo.
A wani bincike da tayi ta gano cewa rashin jituwar dake a tsakanin jaruman biyu ya samo asali ne a wattanin baya tun lokacin da za'a fara shirin fim din Rariya na Rahma Sadau din da aka ce ta gayyaci Nafisa Abdullahi amma taki yadda tayi bayan kuma ta karbar mata makudan kudade.
Binciken namu kuma ya bayyana cewa hakan ne ma ya sanya jarumar Rahma Sadau ta maka Nafisa Kotu domin a bi mata hakkin ta inda daga nan kowa ya ja daga cikin su yana zafafan kalamai ga yar uwar ta.
Source: Naij Hausa
Title :
Nafisat Abdullahi Tayi Kaca Kaca Da Rahma Sadau
Description : Labarun da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni da cewa da alamu takun sakar da ke a tsakanin manyan jarumai mata a masana'antar ...
Rating :
5