A karon farko cikin fiye da shekaru 30, mazauna yankin Gaza da ke Palasdinu sun je gidan kallo wato Cinema.
Gidan kallo na Samer da ke birnin Gaza ne ya haska wani fim na musamman akan yadda Palasdinawa ke rayuwa a gidajen yarin Isra'ila.
Mutane kusan 300 ne suka halarci cinemar domin kallon fim din.
An dai rufe cinemar ta Samer ne tun shekarun 1960, yayinda a shekarun 1980 kuma aka rufe manyan allunan cinemar sakamakon rikicin Intifada da ya barke.
Tun daga wancan lokaci sai dai a rinka nuna fina-finai jefi-jefi a wasu wuraren da ake bayar da haya.
Yanzu haka dai al'ummar Gazan sun ce suna a cigaba da haska fina-finai a Cinemu, saboda debe kewa a nishadi.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutanen Gaza Sunyi Kallo A Cinema Bayan Shekara 30
Description : A karon farko cikin fiye da shekaru 30, mazauna yankin Gaza da ke Palasdinu sun je gidan kallo wato Cinema. Gidan kallo na Samer da ke birn...
Rating :
5