Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti ya rantse cewa Shugaba Buhari yana can rai hannun Allah a Landan har yayi ikirarin yana da hotunan sa. Sai ga shi ashe ba haka abin yake ba.
Tsohon Ministan kasar Femi Fani-Kayode yana cikin wadanda su kace Shugaban kasar ba zai dawo ba. Shi ma dai ya ga ikon Allah.
Shugaban tafiyar Biyafara Nnamdi Kanu a baya yace ta Shugaba Buhari ta kare don ya gama mulki. Kamar dai yadda Babban Faston Ingila J. Welby ya fada addua tayi aiki.
Ana zargin 'Yan Shia da yi wa Shugaban kasar asiri. Wani Dan Majalisa da kan sa ya bayyana wannan kwanakin baya. Wasun su dai sun sha alwashin Shugaban kasar ba zai dawo ba.
Source: Naij Hausa
Title :
Mutanen Dasukaji Kunya Bayan Dawowan Buhari
Description : Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti ya rantse cewa Shugaba Buhari yana can rai hannun Allah a Landan har yayi ikirarin yana da hotunan sa. Sai ...
Rating :
5