Akalla matasa milyan daya da dubu dari biyu ne su ka cike fom, kuma su ka aika neman aiki a Hukumar Shige da Fice ta, kasa, wato Immigration, alhali kuma gaba daya jami’ai dubu da dari biyu ne kacal za a dauka.
A ranar Litinin, shugaban hukumar, Muhammad Babandede ya bayyana cewa mutane 1,112 kacal za a dauka aikin.
Yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai Babandede ya ce za a dauki Mataimakan Sufurtanda na biyu da na uku da kuma Mataimakan Sufeto.
Ya kara da cewa dukkan wadanda ba su cika sharuddan cika shekarun da ake bukata ba, ko kuma wadanda zurfin ilmin su bai kai yadda ake bukata ba, duk za a zabtare sunayen su daga tsarin.
Babandede ya ce tuni sun dauki darasi daga harkallar daukar ma’aikatan da hukumar ta samu kan ta a cikin 2014, inda wasu manema aikin su ka rasa rayukan su a wurin tirmitsitsi.
Dangane da kauce wa haka ne ma ya ce sun dauki matakan kauce wa sake faruwar hakan ta hanyar yin aikin tantancewar kashi daban daban.
Ya kuma sha alwashin cewa ba za a nuna alfarma, sani, sabo ko fifita wani ko wasu a kan wasu ba. Ya kuma tabbatar da cewa ba zai taba yarda wasu manya tankwasa shi wajen kauce wa ka’idar daukar ma’aikatan ba.
Title :
Mutane Miliyan 1.2 Suka Cike Fom Din Aikin Immigration Bayan 1200 Kacal Ake Nema
Description : Akalla matasa milyan daya da dubu dari biyu ne su ka cike fom, kuma su ka aika neman aiki a Hukumar Shige da Fice ta, kasa, wato Immigratio...
Rating :
5