Adadin wadanda suka kamu da cutar Kwalara, ya kai 500,000, tun bayan kasar Yemen ta fada mummunan yaki, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana.
A kalla mutum 1,975 ne suka rasa rayukansu, tun bayan barkewar cutar mai nasaba da rashin tsaftataccen ruwan sha tun a watan Afrilun bana.
Hukumar WHO ta ce mutanen da suka kamu da cutar na samun sauki, amma kuma a kalla mutum 5000 na kumawa da ita a ko wacce rana.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutane Dubu Dari Biyar Ke Fama Da Kwalara A Yemen
Description : Adadin wadanda suka kamu da cutar Kwalara, ya kai 500,000, tun bayan kasar Yemen ta fada mummunan yaki, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya...
Rating :
5