Mutum 12 sun halaka a lokacin wani hatsarin kwale-kwale dauke da fasinja a Legas ranar Lahadi, a cewar gwamnatin jihar, wadda ta dora alhakin hatsarin a kan daukar mutane fiye da kima a cikin jirgin.
Hukumar da ke kula da hanyoyin sufurin ruwa ta jihar Legas ce ta sanar da aukuwar hatsarin, inda ta ce an gano karin gawa uku, lamarin da ya sanya adadin mutanen da suka mutu zuwa 12.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato hukumar tana cewa an kai mutum hudu asibiti kuma suna ci gaba da samun kulawar likita.
Hatsarin ya auku ne a kusa da unguwar Ilashe da ke gabar teku.
Gwamnatin Lagos ta kuma ce rashin bin doka na daga cikin dalilan da suka janyo aukuwar hatsarin.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutane 12 Sun Mutu Ta Hatsarin Kwale Kwale A Legas
Description : Mutum 12 sun halaka a lokacin wani hatsarin kwale-kwale dauke da fasinja a Legas ranar Lahadi, a cewar gwamnatin jihar, wadda ta dora alhaki...
Rating :
5