Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ba za ta sauya matsayarta kan uzurin da ta bayar na cewa beraye ne suka yi barna a ofishin Shugaba Muhammadu Buhari ba, wanda hakan ne ya sa zai dinga aiki daga ofishinsa na gida, bayan dawowarsa daga jinyar wata uku a Landan.
Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriyar, kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu ne ya sake nanatawa BBC wannan batun, inda ya ce, duk wanda ya san Abuja, to ba abin mamaki ba ne don an ce bera sun yi barna a wani waje.
"Ko wanne dan Najeriya yana da damar ya fahimci abu yadda tunaninsa ya ba shi, amma gaskiyar magana ita ce su wadannan beraye sun lalata wayar na'urar sanyaya daki ta ofishin ne daga waje, har suka samu hanyar shiga ciki," in ji Malam Garba Shehu.
Tun bayan fadar shugaban ta bayyana cewa shugaban zai rika aiki daga gida maimakon ainihin ofishinsa, saboda beraye da sauran kwari sun yi barna a ofishin, mutane da dama a ciki da wajen kasar sun yi ta shagube da gugar zana da ma kalamai iri daban-daban na nuna shakku a kan maganar.
Ga dai yadda tattaunawar Malam Garba Shehu ta kasance tsakaninsa da abokin aikinmu Muhammad Kabir Muhammad, kan yadda suke ji sakamakon irin maganganu da kallon da ake musu kan wannan sanarwa da suka yi:
Source: BBC Hausa
Title :
Munanan Kan Bakanmu,Beraye Ne Sukayi Barna A Ofishin Shugaban Kasa
Description : Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ba za ta sauya matsayarta kan uzurin da ta bayar na cewa beraye ne suka yi barna a ofishin Shugaba Muham...
Rating :
5