Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriyar nan da su ka ba wa 'yan kabilar Igbo wa'adi na su bar arewacin kasar kafin ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, sun sanar da janyewar wa'adin da suka bayar .
Hadakar kungiyoyin ta sanar da janye wa'adin ne a wani taro da ta gudanar a Abuja babban birnin tarrayar kasar da yammacin ranar Alhamis.
A dai cikin watan Yuli ne hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Najeriyar suka fitar da wata sanarwa a Kaduna, inda a ciki suka bayar da wa'adi har zuwa ranar daya ga watan Oktoba na 2017.
Sannan, suka kuma nemi 'yan kabilar Igbo da ke arewa da su kuma yankin da suka fito haka ma 'yan arewa da ke yankin na Igbo da su baro wurin
Maganar bayar da wa'adin dai ta kasance wani mayar da martani ga masu kira da kafa kasar Biafra.
Duk da janyewar wa'adin da hadadiyar kungiyar ta yi, ta kuma bayar da wasu sharuda ga gwamanatin tarayyar da kuma gwamnatocin jihohin arewacin kasar baki daya.
Sharudan dai sun hada da cewa gwamnatin tarayya ta tanadi dokar da za ta bayar da dama ga dukkan mai son ballewa a bashi dama, da kuma gurfanar da Kanu a gaban kuliya, sannan duk kamfanonin da ke aiki a arewacin Najeriya, dole su tanadi guraben aiki da kaso 40 cikin 100 wanda za a bawa matasan yankin.
Source: BBC Hausa
Title :
Mun Fasa Korar Yan Kabilar Igbo Daga Arewa
Description : Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriyar nan da su ka ba wa 'yan kabilar Igbo wa'adi na su bar arewacin kasar kafin ranar 1 ga...
Rating :
5