Mukaddashin shugaban kasa,
Yemi Osinbajo na cikin ganawa
tare da shugabannin
hukumomin tasro a fadar
shugaban kasa dake babban
birnin tarayya Abuja.
Ana ganawar ne a shashin
mukaddashin shugaban kasar
dake fadar Aso Rock.
Wadanda suka halarci ganawar
sun hada da shugaban
ma’aikatar tsaro, Janar Gabriel
Abayomi Olinishakin, shugaban
hafsan soji Janar Tukur Buratai
da kuma shugaban hafsan sojin
sama, Mir Marshal Sadique
Abubakar.
Har ila yau wadanda suka
halarci taron sun hada da,
shugaban tsaro na shugaban
kasa, Abba Kyari; mai ba kasa
shawara a harkan tsaro,
Babagana Monguno; ministan
tsaro, Mansur Dan-Ali da kuma
Gwamnan jihar Borno, Kashim
Shettima, da dai sauran su.
Source from rariya