Akwai cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zarah Umar ta yigame da matsalarmace-macen aure, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.
Wata matashiya wadda ba ta wuce shekara 20 ba ta zo ofishina don ba ni labarin halin da ta tsinci kanta ciki.
Yarinya ce sosai da har kusan cikin bacin rai na tilasta mata ta koma makaranta.
Ta fada min cewa shekarta 22 kuma tana da 'ya'ya biyu.
Ta yi aure tana da shekara 19, inda ta auri wani mutum a bisa zabin iyayenta.
Na girma na taso inda na yi imani da yarda da bin zabin iyaye, don haka na yi mamaki me zai sa biyayya ta zama matsala.
Ta cire mayafinta ta nuna min tabo kaca-kaca a jikinta kama daga hannunta da wuyanta da bayanta.
Mijinta ne yake mata wannan dukan saboda wai a cewar mijin ba ta iya girka ba, abin ya firgita ni har na yi tunanin neman mijin nata don na ji ta bakinsa.
Wani abin mamaki da na hadu da shi sai ya nuna min lamarin ba wani gagarumi ba ne a wajensa.
Ya gaya min cewa tuni ya auri wata matar kuma ba shi da ra'ayin tsohuwar matarsa da 'ya'yanta.
Ya shaida min cewa shi fa ya yanke duk wata hulda tsakaninsu don haka ta yi ta kanta kawai.
Zuciyata ta yi matukar nauyi, don haka na fara tunanin nema wa yarinyar nan mafitar da za ta taimaka mata ta tsaya da kafafunta.
Tambayar da ta lullube zuciyata ita ce, "Me ya sa maza ba sa jin wahalar sakin matansu ne?"
Me ya sa al'ummarmu ke nuna halin ko in kula kan al'amuran aure?
Yaya za a yi mutum ya gujewa nauyin da ke kansa kuma al'umma ta nuna ba wani abu ba ne?
Shirin Adikon Zamani zai kawo jerin shirye-shirye kan wannan batu, inda za mu tattauna don amsa wadannan tambayoyi da kuma kokarin kawo mafita don magance yawan mace-macen aure.
Abu ne mai sauki aure ya mutu a arewacin Najeriya saboda kawai gishiri ya yi yawa a miya.
Shin wannan ba abin damuwa ba ne?
Ina farin cikin gabatar muku da Dokta Zahra'u Muhammad Umar ta hukumar Hisba da ke Kano.
Tana da tarin misalai kan irin wadannan matsaloli.
Labarinta da ta ba ni ya sake tsorata ni ba kadan ba kan yadda mutanenmu ke jin saukin yin saki.
Har ina tunanin ko dai dama tun lokacin da za a yi auren ne ba a gina shi kan tafarkin da ya dace?
Ko kuwa dai kawai an mayar da sakin ne abin kwalliya.
Yayin da wasu masu sharhi ke danganta yawan mace-macen aure ga rashin samun tarbiyya tun daga gida, wasu kuwa na dora laifin ne a kan mazajen.
Source: BBC Hausa