Akwai cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zarah Umar ta yigame da matsalar fyaden, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.
Ko wacce wayewar gari, sai an samu labarin aikata fyade a wani waje. Abin ya zama ruwan dare ta yadda fushinmu da babatunmu ba sa wani tasiri.
Abin har ya zama cewa mutane ba sa kaduwa sosai yanzu idan suka ji labarin fyade.
Idan kuwa abin ya shafi yara kanana ne, sai dai mu girgiza kai kawai mu ce Allah ya sauwake.
Muna tambayar kanmu ko me ya sa hakan? Muna tambayar kanmu dalilin da ya sa fyade ya zama ruwan dare a yanzu?
Muna tambayar ko me ya sa yaranmu ba su tsira ba yanzu ko da a cikin gidajenmu yayin da muka bar su da 'yan uwanmu?
Wa za a zarga? Shin hakan na nufin rashin mayar da hankalin iyaye kan sha'anin 'ya'yansu na sa a dinga cutar da yaran ta hayar lalata da su ba tare da sanin iyayen ba?
Na hadu da wata baiwar Allah mai suna Asabe a Kaduna. Wani makwabcinsu dan shekara 38 ne ya yi mata fyade. Mahaifiyarta ta gaya min cewa sun matukar amincewa da wannan mutum.
Ta sawa ranta cewa shi mutum ne mai son yara shi ya sa ba ta taba kawo komai a ranta ba. A takaice ma har a lokacin da ya fara cin zarafin 'yar tata ba ta zarge shi da komai ba, sai da wata makwabciyarta ta jawo hankalinta kan yada halayyar 'yar ke sauyawa da kuma irin jita-jitar da ake yadawa a unguwar.
Da na tambayeta ko ya aka yi ba ta lura ba, sai ta ce min hankalinta ya dauku wajen ganin ta wadata 'ya'yanta da abin da za su rayu na bangaren ci da sha da sutura.
Ina taya iyayen yaran da aka yi wa fyade jaje sosai. Da wahala kwarai mutum ya gane irin halin bakin cikin da suke samun kansu a ciki a yayin da suka gane cewa an zalunci 'ya'yansu.
Babban abin bakin cikin ma shi ne idan har wanda ya aikata hakan dan gida ne.
Me ya sa ake samun karuwar yi wa yara fyade? Hukumomi ne ba sa yin abin da ya dace don ganin an yi adalci?
Masu fyade nawa aka kai kotu aka kuma yanke musu hukunci?
Source: BBC Hausa
Title :
Meyasa Aka Gagara Magance Matsalar Fyade
Description : Akwai cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zarah Umar ta yi game da matsalar fyaden , sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro. K...
Rating :
5