Gwamnatin Najeriya ta ce an kammala dukkannin shirye-shirye na mayar da 'yan matan sakadaren Chibok da aka sako su fiye da 100 wadanda mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014 wurin iyayensu.
Gwamnatin ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ministar kula da harkokin mata ta yi.
Fiye da 'yan mata 200 ne 'yan Boko Haram suka sace, amma sun sako guda 106 a cikin watannin goman da suka gabata.
Ministar matan Hajiya Aisha Jummai Alassan ta ce sai da aka kwantarwa da 'yan matan hankali tare da duba lafiyarsu, a wani shiri na maido da su cikin hayyacinsu da gyara dabi'unsu da gwamnati ta shirya, kafin mayar da su a hannun iyayensu.
Hukumomin sun ce yanzu haka duka 'yan matan su 106, sun murmure ba sa tare da wata damuwa a zukantansu, kuma sun shirya haduwa da iyayensu.
Sannan za su koma makaranta da zarar an mika su a hannun iyayensu da sauran danginsu.
Source: BBC Hausa
Title :
'Yan Matan Chibok Zasu Koma Gurin Iyayensu
Description : Gwamnatin Najeriya ta ce an kammala dukkannin shirye-shirye na mayar da 'yan matan sakadaren Chibok da aka sako su fiye da 100 wadanda m...
Rating :
5