Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar kasar jawabi a safiyar ranar Litinin kwana biyu bayan komawarsa kasar.
A jawabin mai tsawon minti 5.40, shugaban ya yi godiya ga 'yan kasar bisa ga addu'o'in da suka yi masa yayin da shafe kwana 103 yana jinya a birnin Landan.
Har ila yau shugaban ya mayar da martani ga masu fufutikar ballewa daga kasar da batun tsaro da kuma gyara tattalin arzikin kasar.
Sai dai shugaban bai yi karin haske ba kan batun lafiyarsa.
Ga cikakken jawabinsa:
Ya ku 'yan uwana 'yan Najeriya.
Ina mai matukar godiya ga Allah da kuma daukacin 'yan Najeriya saboda addu'o'in da suka yi mini. Ina farin cikin dawowa gida cikin 'yan uwana maza da mata.
Yayin da nake jinya a kasar Birtaniya, ina samun labaran abubuwan da ke faruwa a gida.
'Yan Najeriya suna tattauna al'amuran da suke faruwa, amma na fahimci cewa wasu daga cikin kalaman da ake yi musamman a kafofin sada zumunta sun ketara iyakar dokokin kasar nan inda suke sanya alamar tambaya game da ci gaba da kasancewarmu a matsayin kasa guda. Wannan wani abu ne na wuce gona da iri.
A shekarar 2003 bayan da na shiga siyasa, marigayi Cif Emeka Ojukwu ya taba ziyarta ta kuma ya zauna wurina a Daura.
Mun kwashe fiye da kwana biyu muna tattauna matsalolin Najeriya, a wasu lokutan mukan shafe dare muna magana. A karshe mun cimma matsayar cewa wajibi ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya kuma dunkulalliyya.
Hadin kan 'yan Najeriya wani abu ne da akacimma matsaya a kai. Kuma ba ya bukatar a sake waiwayarsa.
Ba za mu bari wasu marasa dattako su fara tada fitina kuma idan abubuwa suka lalace su gudu su bar wasu da aikin dawo da doka da oda, wata kila ma hakan ba zai yiwu ba sai an zub da jini.
Kowane dan Najeriya yana da 'yancin rayuwa da kuma gudanar da harkokinsa a ko ina a Najeriya ba tare da an yi masa wani shamaki ba.
Na yi amannar cewa dimbin 'yan Najeriya suna da irin wannan tunani.
Sai dai wannan ba yana nufin cewa babu kwararan batutuwan da suke damunmu.
Kowane bangare yana da korafinsa. Amma dadin tsarin da ake tafiyar da kasar a kai yanzu shi ne, yadda ya tanadin hanyoyin da duk wadanda suke ganin an yi musu ba daidai ba, za su iya gabatar da korafinsu da kuma yadda za a ci gaba da tafiya tare.
Majalisar dokoki ta kasa da kuma majalisarkoli ta kasa su ne wuraren da doka ta yarda a tattauna manyan batutuwan da suka shafi Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Marasa Dattako Ke Kalaman Kiyayya-Buhari
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar kasar jawabi a safiyar ranar Litinin kwana biyu bayan komawarsa kasar. A jawabin m...
Rating :
5