Marigayi Gadi Ya Bada Gudummawa Wajen Ciyar Da Jihar Bauchi Gaba, Inji Malam Isa Yuguda
Tsohon gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya yi jimamin rasuwar mataimakinsa a lokacin da yake gwamna, wato Alhaji Garba Muhammad Gadi (Danburam Katagum) wanda ya rasu a ranar Talatar da ta gabata.
Malam Isa Yuguda ya ce ya yi matukar kaduwa a yayin da ya ji labarin rasuwar abokin nasa kuma abokin aikinsa, wanda ya baiyana cewa a yayin da suka yi aiki tare ya bada gudummawa matuka wajen ganin jihar Bauchi ta samu ci gaba.
Tsohon gwamnan na Bauchi wanda ya bayyana hakan a wata takardar da hadiminsa kan fannin yada labarai, Bashir Umar ya rabawa manema labarai a jiya, ya kuma mika sakon ta'aziyyar rasuwar marigayi Gadi ga al'ummar jihar Bauchi baki daya da kuma Masarautar Katagum da ma iyalan mamacin.
Malam Yuguda ya kuma yi fatan Allah ya jikansa ya sa aljanna ce makoma, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.
Title :
Malam Isa Yuguda ya nuna Jimaminsa game da Rasuwan Garba Gadi
Description : Marigayi Gadi Ya Bada Gudummawa Wajen Ciyar Da Jihar Bauchi Gaba, Inji Malam Isa Yuguda Tsohon gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya yi ...
Rating :
5