Wasu mahajjatan Birtaniya su tara sun isa birnin Madinah na Saudiyya a keke, bayan sun yi tafiyar kilomita 3,000 daga London.
Hukumomin Saudiyya sun tarbi mutanen a Madina cike da murna da jinjina a gare su.
Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa kungioyin masu tseren kekuna na Madinah da Taibah ne suka tarbi mahajjatan karkashin jagorancin hukumar wasanni ta Saudiyya, inda aka dinga yi musu kade-kade da watsa musu furanni don nuna farin cikin bajintar da suka yi.
Wani jami'i daga kungiyar masu tseren kekuna ta Taibah, Mohammed Al-Sarani, ya shaida wa Saudi Gazette cewa, "Abin da mahajjata suka yi na zuwa da keke abin a yaba ne."
An bai wa mahajjatan umarnin su isa har Masallacin Annabi SAW da kekunansu.
Mutanen sun bar birnin London na Birtaniya ne a ranar 14 ga watan Yuli, inda suka ratsa ta kasashen Faransa da Switzerland da Italiya da Girka da Masar.
Da farko dai sun so ratsawa ne ta kasashen Turkiyya da Syria da Jordan, amma saboda matsalar tsaro sai suka tafi da jirgin ruwa daga Girka zuwa Masar, inda daga can kuma suka shiga jirgin sama da ya kai su Jiddah.
Daga Jiddah ne suka sake hawa kekunansu inda suka je Madina akai karkashin rakiyar motar 'yan sanda da motocin kungiyar agaji ta Red Cross.
Jagoran matafiyan Abdul Wahid Don White, ya ce, sun shirya tafiyar ce don su nunawa kasashen da suka ratsa a yayin tafiyar cewa Musuluci addini ne na zaman lafiya da juriya.
Kafin su fara bulaguron nasu dai, mahajjatan wadanda 'yan wata kungiyar jin kai ce da ke Birtaniya, sun yi fatan hada kudi fam miliyan daya don taimakawa 'yan Syria da magunguna.
Farkon Tafiyar
Tafiyar ta faro ne daga yankin Gabashin London inda suka tuka kekunansu zuwa New Haven, sai suka hau karamin jirgin ruwa zuwa Dieppe na Faransa.
Daga can suka kara tuka kekuna zuwa Paris, suka wuce Switzerland, suka ratsa Jamus da Austria da Liechtenstein sai suka shiga Italiya.
A birnin Venice ne suka sake shiga karamin jirgin ruwa zuwa Igoumenitsa da ke Girka.
Suka kara hawa kekuna suka fice daga Girka suka hau jirgin sama don wuce teku, suka isa birnin Iskandariya na Masar, suka wuce Hurghada inda suka sake hawa jirgin ruwa zuwa garin Yanbu na Saudiyya.
Abdul Wahid dai ya ce ya fara tunanin yin wannan bulaguro ne shekara 11 da ta wuce a lokacin da ya shiga Musulunc
Source: BBC Hausa
Title :
Mahajjata Tara Sun Isa Madina A Keke
Description : Wasu mahajjatan Birtaniya su tara sun isa birnin Madinah na Saudiyya a keke, bayan sun yi tafiyar kilomita 3,000 daga London. Hukumomin Sau...
Rating :
5