Mukaddashin Shugaban Najeriya ya ce lokaci ya yi da mahukuntan kasar za su aiwatar da matakan shawo kan kalubalen tsaro daban-daban da suka tunkaro kasar a halin yanzu a maimakon maganar fatar baki.
Farfesa Yemi Osinbajo na magana ne yayin wani muhimin taro da dukkanin gwamnoni da shugabannin hukumomin tsaron kasar da aka kira taron koli kan tsaro da tattalin arziki; wanda aka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
Daya daga cikin gwamnonin Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, wanda ya yi wa manema labarai karin bayani kan abubuwan da suka tattauna, ya ce taro ne na tsaro na kasa da aka fadada shi daga taron da aka saba yi na tattalin arzikin kasa.
Source: BBC Hausa
Title :
Maganar Fatan Baki Bazata Magance Matsalar Tsaro A Nigeria Ba
Description : Mukaddashin Shugaban Najeriya ya ce lokaci ya yi da mahukuntan kasar za su aiwatar da matakan shawo kan kalubalen tsaro daban-daban da suka ...
Rating :
5