Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ba Barcelona wa'adin ranar Litinin kan ta fadi kudin da za ta sayi Philippe Coutinho, kamar yadda jaridar Onda Cero ta bayyana.
Arsenal tana shirin sayen dan kwallon Real Madrid Marco Asensio a kan fam miliyan 75 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai ranar Alhamis, in ji jaridar Sunday Express.
Everton tana zawarcin dan wasan Leicester City Jamie Vardy a kan fam miliyan 40, sai dai dan wasan ya son komawa Chelsea ne, a cewar jaridar Sunday Mirror
Har ila yau jaridar ta ruwaito cewa Liverpool ta tashi tsaye kan batun neman Oxlade-Chamberlain, wanda shi ma ake ganin yana son komawa Chelsea.
Arsenal za ta sayar da Kieran Gibbs da Alex Oxlade-Chamberlain da Lucas Perez da Shkodran Mustafi kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai, kamar yadda jaridar Sunday Telegraph ta wallafa.
Kungiyar Juventus tana zawarcin dan wasan tsakiyar Barcelona, Andre Gomes, kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.
Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai fidda rai kan sayen Thomas Lemar daga Monaco da kuma Virgil van Dijk na Southampton ba, in ji jaridar Sun.
Paris St-Germain ta tashi tsaye kan zawarcin Kylian Mbappe a farashin fam miliyan 166 kafin ranar Alhamis, sai dai Monaco ta fi so ta sayar da dan kwallon ga Real Madrid, kamar yadda Sunday Telegraph ta ce.
Source: BBC Hausa
Title :
Liverpool Tabawa Barca Wa'adi Kan Coutinho
Description : Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ba Barcelona wa'adin ranar Litinin kan ta fadi kudin da za ta sayi Philippe Coutinho, kamar yadda ...
Rating :
5