Birnin Legas shi ne birnin da ya fi wuyar rayuwa, baya ga birnin Damascus na kasar Siriya da ke fama da yaki, in ji wani bincike na shekara-shekara.
Daya daga cikin dalilan, in ji binciken na mujallar The Economist, shi ne barazanar da birnin Lagos ke ci gaba da fuskanta daga kungiyoyi kamar na Boko Haram, wanda hakan ke yin kafar ungulu ga samun cikakkiyar kwanciyar hankali.
Cikin watanni shiddan da suka wuce, birane 35 cikin 140 da aka bincika sun yi ta samun sauyi a matsayinsu, amma 12 daga cikinsu sun ci gaba da kasancewa a kasa, kyawun rayuwa a cikinsu na ci gaba da kasancewa kasa da kashi 50 cikin 100.
A yayin da rahoton, wanda sashen bincike na mujallar Economist ya fitar ke nuna cewa biranen Lagos da na Damascus ne basu da saukin rayuwa, a hannu guda kuma ya ce biranen Melbourne na Australiya da Vienna na Austria ne suka fi saukin rayuwa a duniya.
Baya ga Lagos da Damascus, sauran biranen da rahoton ya ambata a matsayin wadanda ba su da saukin rayuwa sun hada da birnin Kiev na Ukraine da Douala na Kamaru da Harare na Zimbabwe da Karachi na Pakistan da Algiers na Aljeriya da Port Moresby na Papua New Guinea da Dhaka na Bangladesh da kuma Tripoli na Libiya.
Source: BBC Hausa
Title :
Lagos Ne Gari Na Biyu Mai Wahalar Rayuwa A Duniya
Description : Birnin Legas shi ne birnin da ya fi wuyar rayuwa, baya ga birnin Damascus na kasar Siriya da ke fama da yaki, in ji wani bincike na shekara-...
Rating :
5