RADE-RADIN SAYAN YAN WASA- LITININ 31/7/2017
1. Manchester United ta kammala sayan dan wasan tsakiya Nemanja Matic mai shekaru 28 daga Chelsea akan £40m a yarjejeniyar shekaru uku. Matic ya zamo dan wasa na uku da United ta saya a kakar wasa ta bana bayan zuwan dan wasan baya Victor Lindelof daga Benfica akan £31m da kuma dan wasan gaba Romelu Lukaku daga Everton akan £75m.
2. Barcelona na tsammanin Neymar zai dawo daukar horo ranar Laraba kuma ta shirya kai karar PSG idan ta biya zunzurutun kudi har £198m wajen sayan Neymar.
3. Barcelona za ta kai tayin £53m don neman sayan dan wasan Arsenal Mesut Ozil mai shekaru 28 idan ta kasa sayan dan wasan Liverpool Philippe Coutinho mai shekaru 25.
4. Chelsea ta shirya cika sharudan da Bayern Munich ta sa don daukar dan wasan tsakiya Renato Sanches mai shekaru 19 a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa.
5. Dan wasan gaban Leicester dan kasar Algeria Riyad Mahrez mai shekaru 26 na fatan Roma za ta sake dawowa da tayi na uku, bayan da Foxes din ta yi watsi da tayinta na £28m da na £32m.
6. Barcelona na duba yiwuwar sayar da dan tsakiyar kasar Portugal Andre Gomes mai shekaru 28 wanda ya zo kungiyar shekarar da ta gabata.
7. Kocin Manchester United Jose Mourinho zai jira har kakar wasa mai zuwa kafin ya nemi dan wasan gaban Real Madrid Gareth Bale mai shekaru 28 akan £90m.
8. Kocin Arsenal Arsene Wenger ya jaddada cewa dan wasan gaba Alexis Sanchez ba zai koma Manchester City ba, kuma yana tsammanin dan wasan zai dawo daukar horo a gobe Talata.
9. Cristiano Ronaldo ya bayyana a gaban kotu yau Litinin bisa zargin da ake yi masa na kin biyan haraji. Hukumomi a kasar Sifaniya na zargin Ronaldo da kin biyan kudin harajin da ya kai €14.7m. Ronaldo ya bayyana hujjojinsa a gaban kotu kafin a dage sauraren karar. Idan aka sameshi da laifi zai iya fuskantar biyan tarar kudi har €28m da kuma zaman gidan yari na shekaru uku da rabi.
Title :
Labari Wasanni
Description : RADE-RADIN SAYAN YAN WASA- LITININ 31/7/2017 1. Manchester United ta kammala sayan dan wasan tsakiya Nemanja Matic mai shekaru 28 daga Chel...
Rating :
5