Mukaddashin shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu ya ce makudan kudaden da hukumar ta samu daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madukwe bai kai cikin cokali ba daga cikin kudaden talakawan Najeriya da ta yi rub da ciki a kan su.
Magu ya ce bayan tsananta bincike kan zargin da ake yiwa ministar, EFCC, ta gano tsabar makudan kudaden da suka kai sama da naira biliyan 47 da kuma wasu Dala miliyan 487 da kuma tarin wasu gidaje da kadarorin da ta mallaka.
Title :
Kudin Da Muka Karba Gun Diezani Somin Tabine
Description : Mukaddashin shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu ya ce makudan kudaden da hukumar ta samu daga...
Rating :
5